in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Talabijin zamani zai karu zuwa miliyan 20 a shekarar 2020 a kasashen Afrika dake kudu da Sahara
2014-01-08 10:06:49 cri

Yawan gidajen da za su amfani da talabijin mai cike da fasahar zamani a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara zai karu da miliyan ishirin tsakanin shekarar 2013 da shekarar 2020, zai cimma miliyan 68, in ji hasashen wani sabon rahoto da Digital TV Research wato cibiyar nazari kan talibiji na zamani ta gabatar a ranar Talata.

Amma duk haka, wannan yana nufin kuma fiye da gidaje miliyan 100 za su cigaba da kasancewa ba tare da irin wannan talabijin ba, kana adadin shigar irin wannan fasahar sadarwa zai cimma kawai kashi 38,4 cikin 100 a shekarar 2020.

A cewar hasashen wannan rahoto game da irin talabiji a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, adadin shigar wannan talabijin zai wuce nan gaba fiye da kashi hamsin cikin dari.

Hakan na nuna damar da ake da a cikin dogon lokaci a wannan shiyya, tare da samun bunkasuwa mai yawa da ake jira da za ta wuce lokacin da aka yi hasashen, in ji Simon Murray, babban mai fashin baki a cibiyar Digital TV Research a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China