Gwamnatin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta, da cibiyar binciken kimiyya ta Sin, da kuma kungiyar habaka ayyukan gona ta jihar Xinjiang, sun gudanar da taron tattaunawa na tsawon kwanaki uku, bisa tushen yin shawarwari da hadin gwiwa, da raya jihar Xinjiang ta hanyoyin kimiyya da fasaha, da kuma neman sabbin hanyoyi gina jihar ta Xinjiang.
Wakilai fiye da dubu daya da dari shida da suka zo daga kamfanoni 41 na cibiyar kula da harkokin kimiyya ta Sin, da birane da kuma larduna guda 11 na babban yankin kasa, da birane na jihar Xinjiang, da kuma jami'o'i, da hukumomin binciken kimiyya, da kamfanonin zamani da abin ya shafa sun hallarci taron. (Maryam).