Shugaba Xi Jinping ya kuma nanata cewa, a halin yanzu an kusa cimma muradun da aka tsara na raya al'ummar Sinawa idan aka kwatanta da sauran lokuta a tarihi, hakan ya sa, ana da kwarin gwiwa sosai bisa na sauran lokuta, don haka ake da imanin cewa, za a cimma wannan buri.
A cewar shugaban, domin cimma wannan muradi, kamata ya yi a nace ga tsarin raya kasa ta hanyar koyar da ilmi da fasaha, da kuma gudanar da aikin kirkire-kirkire tare da nacewa ga bin hanyar raya kasa ta yin amfani da kimiyya da fasaha. Ya kamata a yiwa tsarin horaswa kwaskwarima da shigo da masu zurfin ilmi, a kokarin da ake na horar da ilmi mai zurfi a fannin kirkire-kirkiren masana'antu dake sahon gaba a duniya. (Amina)