Wan Gang ya ce, a shekarar 2008, kasar Sin ta kebe kudin da yawansa ya kai RMB biliyan 20 wajen harkokin nazari, a shekarar 2012, wannan adadi ya kai RMB biliyan 49.8. Yawan manazartan kasar Sin ya kara habaka. Haka kuma, yawan kudaden da aka samu ta hanyar raya sabbin fasahohin zamani ya kara karuwa, har ma ya kai kudin Sin RMB biliyan 10000. Haka kuma, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a wasu fannoni.
Wan Gang ya kara bayyana cewa, yanzu, an shiga wani muhimmin lokaci wajen canja salon raya tattalin arziki, dole ne a yi kokarin kirkiro dabaru kan kimiyya da fasaha, da samun ci gaba a fannin fasahohi na zamani,don kyautata ingancin tattalin arziki.(Bako)