in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika da su gaggauta shiga tsarin amfani da fasahohin zamani
2012-11-08 13:54:00 cri

An gayyaci kasashen Afrika da su gaggauta shiga shirin yin amfani da fasahohin zamani nan da zuwa shekarar 2015, ranar karshe ta wannan tsarin da kungiyar kasa da kasa kan harkokin sadarwa ta tsai da.

Wannan tayi dai ya fito daga bangaren kwararru, masu ruwa da tsaki a aikin jarida da kuma 'yan siyasa a albarkacin wani dandalin kasa da kasa da kungiyar daidaita kafofin watsa labarai na kasashe masu amfani da harshen Faransanci (REFRAM) ta shirya a Dakar daga ranakun 6 da 7 ga watan Nuwamba.

'Ranar 17 ga watan Juni na shekarar 2015, ranar karshe ta fita daga aikin gargajiya zuwa na zamanin da aka tsai da na kuratowa.' in ji shugaban kasar Senegal Macky Sall a yayin bikin rufe taron na karawa juna sani tare yin kira ga kasashen Afrika girmama wannan lokaci da kuma sanya dukkan matakan da suka dace domin shiga wannan zamani cikin nasara.

A nasa bangare, firaministan kasar Senegal, Abdoul Mbaye ya bayyana cewa, cigaban fasahohin zamani na a bakin kofar kasashenmu, ta yadda za'a tabbatar da wannan tsari na tarihi, kuma ya kamata kasashen Afrika su amsa wannan kira yadda ya kamata.

A cewar kwararru, kasashen Afrika da dama na tafiyar hawainiya wajen aiwatar da wannan shirin amfani da fasahohin zamani. Kamar misalin kasashen Djibouti, RDC-Congo, Madagascar, Afrika ta Tsakiya, Burundi da Mauritania da har yanzu ba su nuna wani yankurin a zo a gani ba, in ji mista Justin Aime Tsanga, kwararre fannin ilmin 'yancin sadarwa.

Tsibirin Maurice, Rwanda, Algeria, Maroc, Tunisia sun kasance kasashen da suka samu cigaba a wannan fanni. Haka kuma kwararrun sun bayyana kasashen Nijar, Burkina Faso, Senegal da Mali a cikin kasashen Afrika da suka kafa kwamitin kasa na wucin gadi zuwa amfani da fasahohin zamani da fara samar da sakamako mai kyau. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China