Kungiyar ikon mallakar fasaha ta duniya WIPO ta ba da rahoto a ran 13 ga wata cewa, adadin lambobin kere-kere na kasa da kasa dake neman iznin mallaka ya kai fiye da dubu 200 a shekarar 2013, inda Sin ta maye gurbin kasar Jamus inda ta zama a matsayi na uku, daga cikinsu, kamfanin samar da kayayyakin lantarki na ETZ da kamfnain Huawei suna sahun gaba a duniya.
Kungiyar WIPO ta bayyana cewa, a cikin shekara da ta gabata, saurin karuwar adadin da Sin ta gabatar ya kai sahun gaba a cikin kasashe goma mafi rinjaye a wannan fanni a duniya.
Babban jami'in WIPO Francis Gurry ya bayyana cewa, Sin ta gabatar da dokar ikon mallaka fassaha nan da shekaru 30 da suka gabata, ya zuwa yanzu, yawan adadin lambobin kere-kere dake neman iznin mallaka ya haura na kasar Jamus, abin da ya nuna kwarewar kasar Sin sosai a wannan fanni. (Amina)