Game da batun zaben masu zurfin ilimi da batun yin ritaya da ake sa lura sosai a fadin kasar Sin a halin yanzu, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, akwai bukatar a warware wadannan matsaloli ta hanyar yin kwaskwarima, da kyautata tsarin masu zurfin ilimi, don tabbatar da ingancin tsarin ta yadda za a tabbatar matsayinsu a fagen ilimi.
Kwalejin kimiyya da na injiniyoyi na kasar Sin su ne hukumomin ilmi na koli a fannonin kimiyya, fasaha da kuma fasahohin injiniya. Masu zurfin ilimi na kwalejojin biyu sun kware a wadannan fannoni. An zabe su daga cikin masu binciken kimiyya mafi kwarewa a cikin gida da waje, kuma ana kara zaben sabbin kwararru ne a bayan shekaru biyu biyu. (Zainab)