Mahukunta a tarayyar Najeriya, na daukar matakan samar da wata doka, wadda za ta tabbatar da kiyaye nagartar irran abinci, da ake tagwaitawa a cibiyoyin binciken kasar.
Hakan, a cewar ministar ma'aikatar muhallin kasar Laurentia Mallam, zai taimaka, wajen ganin nau'in irran da ba su da hadari ne kawai, za a yi amfani da su a kasar.
Laurentia ta ce, gwamnatin tarayyar kasar, da hadin gwiwar sauran hukumomin da abin ya shafa, za su fara gudanar da wani shirin wayar da kai, wanda zai baiwa cibiyoyin binciken kasar damar sanin inda aka sa gaba. Baya ga manoma, da ma daukacin al'ummar kasar da ake sa ran shirin fadakarwar zai amfana.
A ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2011 ne dai majalissar dokokin kasar ta amince, da dokar da ta shafi wannan sashi na kariya ga fasahar sarrafa irrai, dokarar da yanzu haka take jiran rattaba hannun shugaban kasar. (Saminu)