in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta hanyar kimiyya da fasaha
2014-01-14 16:08:51 cri

A ranar 13 ga wata, a nan birnin Beijing, yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ke ganawa da babbar edita ta mujallar kimiyya ta Amurka Marcia McNutt, ya bayyana cewa, raya harkokin kimiyya da fasaha na da muhimmanci sosai wajen raya tattalin arziki da daukaka ingancinsa, kasar Sin za ta zurfafa aikin yin gyare-gyare, domin ci gaba da raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta hanyar yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya.

Mista Li ya bayyana cewa, a cikin shekarar da ta gabata, Sin ta kyautata manufofinta daga manyan fannoni, kana ta haye wahalhalu da kalubale da ke gabanta, da cimma burin raya tattalin arziki, cikinsu raya kimiyya da fasaha ya taka rawar a zo a gani. A karkashin sabon yanayin da ake ciki, kasar Sin za ta karfafa aikin yin gyare-gyare, da canja tsarin da ake gudanarwa a yanzu, don raya tunanin mutane wajen ingiza aikin kirkiro da sabbin abubuwa, kana da ci gaba da raya tattalin arziki cikin dogon lokaci da raya zamantakewar al'umma ta hanyar kimiyya da fasaha.

A nata bangare kuma, Marcia McNutt ta taya murna ga kasar Sin da ta cimma burin harbar kumbon Chang'e-3 zuwa duniyar wata, kuma tana fata Sin za ta kara samun babban ci gaba wajen binciken sararin samaniya. Ta ce, Sin ta dora muhimmanci sosai game da kimiyya, kuma ta yi amfani da kimiyya da fasaha don raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da magance batun sauyin yanayi, da gurbata muhalli da sauransu, ta kuma ci gaba da hadin gwiwa a fannin kimiyya da sauran kasashen duniya, don kara horar da kwararru ga kasashe masu tasowa, abin da zai kawo dauwamammen ci gaba ga kasar Sin da kasashen duniya baki daya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China