Masu fashin baki na ganin cewa, wannan yunkuri, wata alama ce da ke bayyana kudurin shugabannin na kasancewa kusa da talakawa tare da nemon hanyoyin samun ci-gaba.
A ranar Litinin ne mambobin hukumar kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS suka ziyarci yankin sai da kayayyakin kere-kere na Zhonggunancun da ke arewa maso yammacin birnin Bejing, wanda a halin yanzu yake kunshe da fitattun kamfanoni kere-kere kimanin 20,000 bayan shekaru 20 da kafa shi.
Mambobin hukumar kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, karkashin jagorancin babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS mista Xi Jinping ne suka ziyarci yankin, inda suka duba kayayyaki dabam-dabam a yankin na Zhongguancun, kana suka tattauna da shugabanni da masana harkokin kimiyya game da dabarun bincike da aiwatar da sabbin fasahohin kimiyya, kamar bangaren kirkire-kirkire, tagwaita tsirrai, sinadarai da sauransu.
A jawabinsa shugaba Xi Jinping ya jaddada muhimmancin kimiyya da fasaha ga ci-gaban kasa, yana mai cewa, kirkire-kirkire, batu ne da ya zama ruwan dare a duniya, kuma abu ne da ake bukata a cikin kasa.
Don haka, ya ce, "wajibi ne mu kara ilimantar da jama'a game da kalubalen da ka iya tasowa kana mu yi amfani da damar da muka samu a bangaren kimiyya da fasahar kere-kere". Ya ce, kamata ya yi kasar Sin ta mayar da hankali wajen hade harkokin bincike da raya tattalin arziki da ci-gaban rayuwar jama'a, karfafa harkokin bincike masu zaman kansu, inganta fasahar ci-gaba, samar da manufar da ta dace da kara bude kofa, huldar kasa da kasa a bangaren kimiyya da fasahar kere-kere. (Ibrahim)