in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin Xi Jinping ya yi jawabi a taron fasahohin injiniya na kasa da kasa na shekarar 2014
2014-06-03 15:49:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi mai taken "Maida fasahohin injiniya hanyar amfanar al'umma, da samar da kyakkyawar makoma", yayin taron fasahohin injiniya na kasa da kasa na shekarar 2014.

A cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a Talatar nan, ya ce gudanar da taron fasahohin injiniya a nan birnin Beijing, abu ne mai kyau da zai inganta fasahohin injiniya na kasar Sin da ma duniya baki daya.

Ya ce, a cikin shekaru fiye da 60 da suka gabata da kafuwar kasar Sin, musamman a cikin wadannan shekaru fiye da 30 na baya bayan nan, da bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, an samu bunkasuwa cikin sauri, a fagen tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar. A ciki, aikin da ke da nasaba da fasahohin injiniya ya taka muhimmiyar rawa.

Kasar Sin tana da kwararrun injiniyoyi fiye da miliyan 42, wadanda ke ba da muhimmin tasiri kan taimaka mata wajen cimma kyakkyawar makoma. A halin yanzu dai, inganta fasahohin kimiyya ta kasance wani muhimmin aiki ga dan Adam wajen tinkarar kalubalen duniya, da kuma cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa. Hakan dai ya sa lokaci ya yi a kara inganta fasahohin injiniya da kirkire-kirkire.

A daidai gabar da jama'ar kasar Sin ke karfafa burin wanzuwar zaman lafiya, da begen samun bunkasuwa, kasar za ta inganta hadin gwiwa, da mu'amala a fadin duniya a wannan fanni, tare da yin kokari tare da kasashen duniya domin warware matsaloli, da kago kyakkyawar makoma tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China