Aiki da fasahar zamani zai iyar taimakawa nahiyar Afrika wajen cimma burinta na tabbatar da tsaro da samun wadatar abinci, a cewar wasu kwararrun kasashen Afrika dake taro tun ranar Alhamis a birnin Dakar na kasar Senegal.
A cewarsu, canja salon tattalin arziki domin kai ga manufar tsaro da samun wadatar abinci tare da rage talauci na nufin ba da himma wajen zamanintar da aikin noma da ba da karfi ga zanarin kimiyya.
Kwararrun na gudanar da wani taron kara wa juna sani na kasa da kasa bisa jigon "canja salon tattalin arzikin yammacin Afrika, wace manufa domin tsaro da samun wadatar abinci tare da rage talauci".
Wannan salo na kawo sauyi, na farko shi ne canja tsarin sarrafawa tare daba himma, da zamanintar da aikin noma. Wato ta yadda za'a samu karfi wajen sarrafawa da ba da karfi ga yin takara, in ji dokta Macoumba Diouf, darektan cibiyar binciken ayyukan noma ta kasar Senegal (ISRA).
Mista Diouf ya kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar Senegal ta amince da kebe kudin Sefa biliyan 3,5 cikin wannan shekara domin sake gina da sake bude cibiyoyi da tashoshin nazarin irin noma.
Shi kuma shugaban kwamitin zartaswa na cibiyar kasa da kasa ta binciken manufofin cimaka, Fawzi Al-Sultan, cewa ya yi, idan ana maganar matsayin bincike wajen kara samun albarkatun noma, to shi ne ana nufin taimakawa jama'a wajen karfafa matsayinsu na kyautata aikin gonarsu. (Maman Ada)