'Yan sandan lardin Diyala dake gabashin kasar Iraqi sun ce dakarun rundunar tsaron kasar sun yi arangama da mayakan kungiyar ISIS dake yunkurin mamaye mafiya yawan biranen kasar dake lardin.
Rundunar tsaron ta kuma ce dauki ba dadin na ranar juma'a, ya tilasawa mayakan sa kan masu adawa da gwamnati ja baya, ko da yake har ya zuwa yanzu su na ci gaba da rike birane biyu da suka mamaye.
A wani ci gaban kuma shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya bayyana cewa Amurka ba za ta tura sojojin ta zuwa Iraqi domin yaki da masu tada kayar baya ba, a maimakon haka a cewar sa za su bada duk wani tallafin ga sojojin kasar ta Iraqi, hakan kuma zai danganci irin matakin da mahukuntan Iraqin za su dauka, wajen warware rikicin kasar a fannin siyasa. (Amina)