A gun taron manema labaru da aka shirya bayan ganawa tsakanin Ban Ki-moon da firaministan kasar Iraqi Nuri Al-Maliki, Mr. Ban ya yi Allah-wadai da harin ta'addanci da ake kai wa fararen hula, musamman ma, ya fi nuna damuwa sosai game da tsanantar rikicin da aka samu a lardin Anbar. Jami'in na MDD ya yi kira ga hukumomin kasar Iraqi da su gudanar da bincike domin gano dalilin barkewar rikici dake tsakanin sojojin gwamnati da dakaru masu dauke da makamai na lardin. A sa'i daya kuma, ya yi kira da a koma kan teburin shawarwarin siyasa domin bullo da bakin zaren warware wannan rikicin.
A nasa bangare kuma, Maliki ya bayyana cewa, rikicin da aka samu a lardin Anbar ba matsala ce ta harkokin cikin gida na kasar Iraqi ba, ya jaddada cewa, gwamnatin Iraqi ba za ta yi shawarwari da dakarun dake dauke da makamai ba.
Tuni, jami'an gwamnatin Iraqi sun bayyana cewa, a cikin makwanni biyu da suka gabata, rikicin dake tsakanin sojojin gwamnatin da mayakan kungiyar Al-Qaeda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 60, tare da jikkatar wasu kimanin 300. Kwamitin sulhu na M.D.D. da Ban Ki-moon sun ba da sanarwar yin Allah wadai da tashe-tashen hankulan da suka faru a lardin Anbar.(Bako)