A wannan rana, an kai wa rundunar sojan tsaron kasar ta Iraqi hare-hare lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 27, yayin da 41 suka jikkata.
Bugu da kari, hari mafi muni da 'yan ta'adda suka kaiwa rundunar sojan tsaron kasar ya faru a kan hanyar arewaci da ke da nisan kilomita dari biyu daga babban binin kasar, Bagadaza,inda wasu masu dauke da makamai da ba a san su wane ne ba suka bude wuta da bindigogi kan rundunar sojan tsaron kasar wadanda suke kula da na'urorin man fetur, harin da ya yi sanadiyar mutuwar 'yan sanda guda 11
Ban da hare-haren da 'yan ta'adda suka kai wa rundunar sojan kasar, sun kuma kai wa fararen hula hare-hare a garin Maqdadiyah da ke arewa maso gabashin birnin Bagadaza, da kuma lardin Salahuddin dake arewacin kasar ta Iraqi, abin da haddasa mutuwar mutane guda 33.
Ya zuwa halin yanzu, babu wanda ya sanar da daukar alhakin hare-haren.