in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren da aka kai a Iraqi sun yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 12
2013-05-13 15:02:45 cri
A ranar 12 ga wata, an kai wasu hare-hare a wurare da dama a kasar Iraqi, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 12.

Wani dan sanda da ba ya son fayyace sunansa ba ya bayyana cewa, 'yan sanda sun gano gawawwaki 5 a Hamam al-Alil dake kudu da birnin Mosul hedkwatar lardin liwa-al-neineva a yankin arewacin kasar, kuma yayin da aka gano gawawwakin, an same su da ankwa da marufin idanu, tare da harbin bindiga da dama a jikinsu.

Bisa labarin da wani jami'in ma'aikatar kula da harkokin cikin gida na Iraqi ya bayar, an ce, wani mutum mai dauke da bindiga ya bude wuta kan wasu gungun mutane a garin Mashahda, da ke da nisan kilimita 40 a arewa da birnin Bagadaza, hedkwatar kasar, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 3. Ban da wannan kuma, wasu masu dauke da bindiga 2 sun kutsa kai cikin wani gida da ke unguwar Karrada dake cibiyar birnin Bagadaza, inda suka kashe mata guda 4 a wurin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China