'Yan sandan kasar Iraqi sun bayyana a ranar Alhamis 16 ga wata cewa, an kai hare-hare sau da dama a wassu sassan kasar, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 30, yayin da wasu 25 suka jikkata.
An ba da labari cewa, a wannan rana, an kai hare-haren boma-bomai ko bindigogi a kalla 6 a wuraren dake kewayen birnin Baghdad, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 9, yayin da wasu mutane 20 suka samu raunuka.
A wannan rana da yamma, rundunar 'yan sanda dake sintiri ta gano gawawaki 14 a wani lambu dake kusa da garin Mshahada dake tsakiyar kasar Iraqi. Ban da haka, an kai hare-hare sau da dama a lardin Diyala dake gabashin kasar, lardin al-Anbar dake yammacin kasar da dai sauran larduna, abin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 7 yayin da wasu 5 suka ji rauni. Amma har zuwa yanzu, babu wani mutum ko kungiya da ya sanar da daukan alhakin lamarin.
Ban da harin da aka kai a ran 16 ga wata, an samun hare-hare a ran 14 ga wata a kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 24, yayin da wasu 55 suka raunana. A ran 15 ga wata kuwa, an samun karin wassu hare-hare sau da dama, abin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 70, sannan wasu 147 suka ji rauni.
Idan ba a manta ba, tun farkon shekarar bara, aka rika samun hare-hare a kasar Iraqi, hakan ya sa kasar ta fuskanci kalubale mai tsanani. Bisa rahoton da tawagar tallafin kasar Iraqi ta MDD ta bayar, an ce, a cikin shekarar da ta gabata, yawan mutane da suka mutu sakamakon hare-hare ya kai 8,868, daga cikinsu, 7,818 fararen hula ne, ban da haka, mutane fiye da dubu 18 sun ji rauni, adadin da ya kai matsayin koli a shekarun da suka gabata. (Amina)