An ce, jimillar mutanen da maharan suka yi garkuwa da su ta kai 49, cikin hada da babban jakadan ofishin.
Tuni dai babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, da kwamitin tsaron MDD suka yi Allah wadai da wannan lamari, tare da bukatar dakarun da su gaggauta sakin wadannan ma'aikata da iyalansu.
Bugu da kari, a yayin taron shawarwarin da wakilan babban taron MDD karo na 68 ya yi a wannan rana, Ban Ki-moon ya yi kira ga gwamantin kasar ta Iraqi, da kasashen yankin da su hada kai da ragowar kasashen duniya don ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan ta'asa, tare da zage damtse wajen ganin an kiyaye rayukan wadanda aka yi garkuwar da su.
A daya bangaren kuma, kwamitin tsaron ya ba da wata sanarwa ta kafofin watsa labarai, dake kunshe da Allah wadai ga dukkan aikace-aikacen tada tarzoma, da mayakan wannan reshe na kungiyar Al-Qaeda ke yi a kasar ta Iraq, ciki hadda kai hare-hare ga fararen hula, da jami'an tsaro, da mamaye karamin ofishin jakadancin kasar Turkiyya da gine-ginen gwamnatin kasar.
Sanarwar ta kara yi tir da mayakan wannan kungiya game da yin garkuwa da ma'aikatan karamin ofishin jakadancin kasar Turkiyya, da kuma kara yawan 'yan gudun hijira a kasar da dai sauransu.
Tun dai a ranar 10 ga watan nan ne dakaru masu adawa da gwamantin kasar ta Iraqi, suka mamaye birnin Mosul dake arewacin kasar. Lamarin da ya sanya firaministan kasar Nouri Al-Maliki sanarwar kasancewa cikin shirin kota-kwana a dukkanin fadin kasar, tare da yin kira ga majalisar dokokin kasar, da ta sanar da shirin daukar matakan gaggawa a duk kasar domin fuskantar kalubalolin da ka iya bijirowa.
A wani labarin kuma, yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin madam Hua Chunying ta bayyana cewa, da babbar murya Sin ta yi Alahwadai da wannan danyen aiki na ta'addanci.
Yayin da take amsa tambayoyin 'yan jarida a gun taron manema labaru a wannan rana, madam Hua ta furta cewa, yanzu akwai damuwa sosai kan halin da ake ciki a Iraki. Kuma ana ganin cewa, kamata ya yi a saki wadannan mutanen da aka yi garkuwa da su nan take ba tare da shata wani sharadi ba.