A wannan rana da sanyin safiya, an kai wani mummunan hari, inda gungun dakaru 'yan sunni suka shiga wani kauyen 'yan Shi'a mai nisan kilomita 40 da ke kudu da babban birnin kasar Bagdaza, inda suka harbe fararen hula 'yan Shi'a kimanin 16, cikinsu har da yara guda 6. Ban da wannan kuma, a wannan rana da safe, an kai hare-haren boma-bomai 3 da aka dasa a gefen hanya a garin Tarmiyah da ke da nisan kilomita 40 da ke arewa da birnin Bagdaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 5, tare da jikkatar wasu 7.
A hakika dai, a ranar 3 da dare, a cikin sa'o'i biyu kawai, an kai hare-haren boma-bomai 11 a unguwar 'yan Shi'a da ke birnin Bagdaza, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 67, tare da jikkatar wasu sama da 200. Duk da cewa, ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar ta dauki alhakin kai hare-haren, amma, jama'a suna zato cewa, sashen kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaeda da ke kasar Iraqi ya kai wadannan hare-hare.(Bako)