Wasu hare-hare da aka kaddamar a kasar Iraqi a ran 28 ga wata, sun yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 23, yayin da kuma wasu 43 suka jikkata.
Hari mafi tsananin a cewar rundunar 'yan sandan kasar, ya auku ne a lardin Saladin dake arewacin kasar, inda Musulmai mabiya darikar Sunni ke da rinjaye. An ce wasu dakarun sa kai sanye da tufafin rundunar tsaron kasar, sun kafa shingayen binciken ababen hawa dake ratsa wannan yanki, suka kuma harbe mutane 6 dake cikin motoci 2.
Ban da haka, an ce harin kunar bakin wake, da harin boma-bomai da aka dana a motoci sun haddasa mutuwar mutane 3, yayin da wasu 9 kuma suka sami raunuka a birnin Tikrit hedkwatar lardin Saladin. Har ila yau an kai hari ga birnin Tuz Khourmatu, da Shirqat dake wannan lardi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4, da jikkata wasu mutum biyu.
Bugu da kari hare-haren da aka kaddamar a wajen birnin Bagadaza, su ma sun yi sanadin mutuwar mutane 10, yayin da wasu 32 suka samu raunuka.
Amma, har zuwa yanzu, babu daidaikun mutane ko kungiyar da ta sanar da daukar alhakin aiwatar da wadannan hare-hare. (Amina)