Wani jami'in rundunar 'yan sanda da ya son a fadi sunansa ba ya bayyana cewa, manyan hare-haren da aka kaddamar a ranar Talata 3 ga wata, sun auku ne a birnin Bagadaza. A wannan rana da magariba an kai hare hare har sau 11 a unguwoyi da dama na birnin ta hanyar fashewar bomabomai cikin motoci, a wani hari daban kuma an dasa bomabomai a gefunan hanya. Rahotannin da aka samu sun tabbatar da cewa, yawancin unguwoyin birnin da aka kai musu hare haren inda tarin mabiya darikar Shi'a ne ke zaune, wadanda kuma hakan ya haddasa mutuwar mutane a kalla 47, baya ga mutane 163 da suka jikkata.
A wannan rana da safe kuma, wasu karin boma-boman sun tashi cikin motoci, an kuma ji karar harbe-harben bindogogi a cikin birnin Bagadaza ko kuma waje da shi, da kuma lardin Diyala da ke gabashin kasar, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 9, yayin da wasu 7 suka ji raunuka. (Maryam).