in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD yayi maraba da gudanar zaben 'yan majalisu a Iraqi
2014-05-01 16:14:18 cri
Kwamitin tsaron MDD ya yi maraba da gudanar zaben kujerun majalissun dokokin kasar Iraqi a kan lokaci, yana mai kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a fagen siyasar kasar, da su hada karfi da karfe wajen tabbatar da kafuwar gwamnatin da za ta kasance karbabbiya ga daukacin al'ummar kasar.

Cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin na karba-karba Joy Ogwu ya karanta, kwamitin tsaron ya kuma yabawa al'ummar kasar ta Iraqi bisa nuna halin dattaku, yayin kada kuri'un wannan babban zabe da ya gudana a jiya Laraba.

Wannan ne dai karon farko da ake gudanar da babban zabe a kasar ta Iraqi, tun bayan janyewar sojojin sojojin Amurka daga kasar a shekarar 2011. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China