Mataimakin manzon musamman na sakatare janar na M.D.D. game da batun kasar Iraqi George Bustin ya ce, yanzu, aikin da ke gaban kome ga gwamnatin Iraqi shi ne, a ba da kulawa ga wadanda suka jikkata, da tabbatar da tsaronsu. Haka kuma, ya bukaci gwamnatin da ta gaggauta kafa wani kwamitin bincike, don bin bahasin abin da ya faru, da sanar da jama'a game da abin da ya faru.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Iraqi ya bayar, an ce, a wannan rana da sanyin safiya, rundunar tsaro ta Iraqi ta dauki matakan soji a sansanin 'yan gudun hijira na Ashraf, wato inda kungiyar jihadi ta Iran PMOI ke zaune, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19, tare da jikkatar wasu 30. Kungiyar PMOI ta ba da wata sanarwa, inda ta yi Alla-wadai da gwamnatin Iraqi da daukar wannan mataki, kuma abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 52, cikinsu har da manyan jami'ai da dama na kungiyar. Yanzu, gwamnatin Irak ba ta mayar da martani a hukunce ba.(Bako)