'Yan sandan kasar Iraqi sun bayyana a ran 12 ga wata cewa, an kai hare-hare sau da dama a tsakiya da kuma arewacin kasar, inda lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 30, yayin da wasu 104 suka raunana.
Wani majiya wanda bai bayyana sunansa ba ya ce, wani mutum ya kai harin kunar bakin wake a wani dakin shan Kofi a garin Balad na ka'idar Shite dake da nisan kilomita 80 daga birnin Bagadaza, inda fashewar bom din ta lalata shagon, kuma ya haddasa mutuwar mutane a kalla 23 kana wasu 66 suka ji rauni.
Ban da haka, an kai hari a wani kantin sayar da ganyen lambu da 'yayan itatuwa a birnin Baqouba hedkwatar jihar Diyala, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 4, kuma mutane 25 suka jikkata. A birnin Masul kuwa, dake da nisan kilomita 400 daga birnin Bagadaza, masu fafutuka sun kai hari kan wata motar soja, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji uku, kuma sauran biyu suka ji rauni.
Ban da haka, an kai hare-haren bom-bomai sau da dama a lardunan Diyala da Nineveh, wadanda suka yi sanadin jikkatar mutane 11.
An ba da labari cewa, tun farkon wannan shekara, ake fama da hare-hare, inda hakan ya sa an shiga mawuyacin halin tsaro a kasar. (Amina)