Dangane da lamarin, a yayin ziyararsa a kasar Spain, babban sakataren kungiyar NATO Anders Fogh Rasmussen ya bayyana a ranar 12 ga wata cewa, kungiyar ba za ta shiga harkokin kasar Iraqi ba, domin ba ta samu ikon shiga harkokin kasar ba, kuma ba wanda ya taba gabatar wa kungiyar roko domin ta ba da taimako a kan wannan al'amari.
Kaza lika, bayan ganawarsa tare da firaministan kasar Australia Tony Abbott, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a kasar Amurka, shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya bayyana wa kafofin watsa labarai a fadar White House cewa, tawagarsa na nazari kan yadda za a baiwa kasar Iraqi taimakon da ya kamata, tare da daukar duk matakin da ya dace, a game da lamarin kasar ta Iraqi. Kana, a yayin taron manema labaran da aka saba yi, kakakin fadar White House Jay Carney, ya jaddada cewa, kasar ba za ta aike da rundunar sojojin kasa zuwa kasar Iraqi ba. Bugu da kari, ministan harkokin wajen kasar John Kerry ya bayyana cewa, shugaban kasar zai zartar da kuduri kan halin Iraqi a cikin sauri.
A wannan rana kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta sanar da gargadi, inda ta yi kira ga 'yan kasar Turkiyya, wadanda ke zama a kasar Iraqi da su koma kasar Turkiyya da sauri.
A wata sabuwa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin madam Hua Chunying ta bayyana a yau cewa, Sin tana mai da hankali sosai kan yanayin tsaron da ake ciki a Iraki. Kuma Sin tana nuna goyon baya ga kokarin gwamnatin Iraki na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, da fatan jama'ar kasar za su samu zaman lafiya da kwanciyar hankali tun da wuri.