An ce an kaddamar da hare-haren ta'addanci a garin Al-Alam da ke yankin gabashin birnin Tikriti, hedkwatar lardin Saladin da ke arewacin kasar ta Iraqi, da garin Garma da ke kusa da birnin Baqouba, hedkwatar lardin Diyala da ke yankin gabashin kasar, da garin Abu Ghraib da ke yamma da birnin Bagadaza hedkwatar kasar, da garin Riad da ke da nisan kilomita 250 a arewa da birnin Bagadaza.
Har ila yau a yammacin ranar, an harbe magajin birnin Fallujah, dake yankin tsakiyar kasar Iraqi Adnan Hussain, yayin da yake rangadin wani aiki na gwamnatin, a yankin Jubail dake cibiyar birnin,.
Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko mutum da ya dauki alhakin kai wadannann hare-haren.(Bako)