Shugaban kasar Botswana Ian Khama ya jaddada a ranar Laraba niyyar gwamnatinsa wajen kawar da talauci a cikin kasar.
"Mun daura damarar yaki da talaucin dake haddabar kasar.mu." in ji shugaba Kham a cikin wani jawabinsa zuwa ga al'ummar kasar albarkacin bukukuwan krismeti.
A cewar wasu alkaluman kasar, sun bayyana cewa, kimanin kashi 6,5 cikin 100 na al'ummar Botswana, wato mutane miliyan biyu ke rayuwa akalla da dalar Amurka guda a ko wace rana idan aka kwatanta da na shekarar 2002 dake kashi 23,4 cikin 100.
Matsalar rashin aikin yi ita ce babban dalilin dake janyo talauci a kasar Bostwana, adadinsu ya kai kashi 17,8 cikin 100 a wannan kasa.
Yawancin al'ummar Bostwana na ba da karfi ga aikin gona, to sai dai rashin samun ruwan sama cikin lokaci dalilin canjin yanayi ya kara janyo talauci ga mutanen Bostwana.
Kudaden shiga da gwamnatin kasar ta samu sun ja da baya, dalilin faduwar kasuwar lu'u lu'un tun bayan barkewar ricikin kudin kasa da kasa a shekarar 2008, lamarin da ya rage azamar gwamnatin kasar kan kokarin da take na kawar da talauci. Domin yaki da talauci, gwamnati na dukufa wajen bunkasa tattalin arziki mai karko da kuma kafa wani tsarin gina kasa, in ji shugaba Khama, tare da jaddada cewa, dalilin haka ne gwamnatin kasar ta aiwatar da wasu tsare-tsare a wannan fannin na hanyar ba da tallafin kudi ga kananan masana'antu, taimakawa noma, samar da ilmi da kiwon lafiya ga 'yan kasa kyauta, samar da abinci ga dalibai, taimakawa nakasassu da samar da guraben aikin yi. (Maman Ada)