Sin na fatan kasashe daban-daban su ba da gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiya da karko a yankin Asiya-Pacific
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana a nan birnin Beijing a ran 28 ga wata cewa, al'ummar kasashen da ke yankin Asiya-Pacific suna fatan samun zaman lafiya da bunkasuwa, da yin hadin gwiwa da kawo moriyar juna. Don haka, Sin na fatan wadannan kasashe da abin da shafa su ba da gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiya da karko da wadata a yankin.
Ban da haka kuma, game da rikicin da ke faruwa a Ukraine Mr Qin ya nuna cewa, yanke duk wani hukunci ba zai taimaka wajen warware al'amarin ba, illa ya tsananta halin da ake ciki yanzu, wanda bai dace da moriyar bangarori daban-daban ba. (Amina)