Taron ya cimma ra'ayi daya game da batun gyaran tsarin mulkin kasa ta yadda zai iya kiyaye moriyar bangarorin da abin ya shafa, tare da kuma aiki da ra'ayoyin bangarorin da abin ya shafa, sa'an nan ya kamata kananan hukumomi da jam'iyyun siyasa na Ukraine su fara shawarwari tsakaninsu tun da wuri. Bugu da kari, bangarorin hudu sun jaddada muhimmancin kyautata harkokin tattalin arziki da sha'anin kudi yadda ya kamata a kasar Ukraine, haka kuma sun kuma amince da ci gaba da yin shawarwari game da yadda za a aiwatar da wadannan batutuwa tsakanin bangarorin da abin ya shafa.
Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa a ran 17 ga wata, inda ya nuna maraba da sakamakon da taron ya cimma. (Maryam)