Sojojin gwamnatin kasar Ukraine sun dauki matakin musamman a yankin Slavyansk a ranar 24 ga wata, inda suka lalata wasu sansanonin uku da masu goyon ballewa daga kasar Ukraine suka mamaye, tare da harba masu zanga-zanga biyar har lahira. A sa'i daya kuma, kwamitin tsaron kasar ya sanar da cewa, zai gudanar da aikin yaki da ta'addanci a gabashin kasar bisa mataki-mataki.
A wannan rana, ministan tsaron kasar Rasha Sergey Shoigu ya sanar da cewa, sojojin kasar Rasha dake yankunan yammaci da kudancin kasar dake dab da kasar Ukraine sun fara atisayen soja.
Dadin dadawa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ta ba da wata sanarwa a ran 24 ga wata, inda ta nemi Rasha da ta yi bayani kan atisayen soja da ta yi a kan iyaka.
A wannan rana da dare, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ba da sanarwa cewa, ya kamata Amurka ta yi wa mahukuntan Kiev matsin lamba , domin su daina daukar matakan soja a kudu maso gabashin kasar Ukraine. Hakazalika, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a ran 24 ga wata cewa, ya kamata, Ukraine ta bullo da shawarwari tsakanin al'ummar kasarta domin warware rikicin da ake ciki yanzu. (Amina)