in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaron kasar Ukraine ta dauki matakin yaki da ta'addanci a gabashin kasar
2014-04-13 20:44:07 cri

Ministan harkokin cikin gidan wucin gadi a kasar Ukraine Arsen Avakhov, ya ce rundunar tsaron kasar ta fara daukar matakan yaki da ta'addanci a birnin Slaviansk na jihar Donetsk dake gabashin kasar, domin dakile ayyukan 'yan ta'adda, dake ta da zaune tsaye a 'yan kwanakin nan.

A cikin wani rahoton da ya fitar kan shafin yanar gizo, Avakhov ya ce, cibiyar yaki da ta'addanci ta hukumar tsaron kasar Ukraine ce ke jagorantar wannan aiki, da hadin gwiwar ragowar sassan jami'an tsaron kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China