in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin yace tattaunawa ce kadai za ta warware matsalar Ukraine
2014-04-15 20:52:56 cri
Ministan Harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya jaddada cewa warware matsalar da kasar Ukraine take fuskanta sai ta hanyar tattaunawa kadai za'a iya shi maimaikon fito na fito.

Mr Wang ya bayyana hakan ne a yau Talata a nan birnin Beijing lokacin wani zantawa da manema labarai na hadin gwiwwa bayan wata ganawar da yayi da takwaransa na kasar Rasha Sergev Lavrov wanda ya kawo ziyarar aiki.

Yace Kasar Sin na maraba da kokarin tattaunawa akan batun tsakanin kasashen Rashan,Amurka,kungiyar tarayyar Turai da ita kanta Ukraine din,wanda a cewar sa hanya mafita shine a tattauna game da abinda zai kawo alfanu ga dukkan bangarorin da hakan ya shafa.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China