in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne a daidaita batun Ukraine a siyasance, in ji kasar Sin
2014-04-17 17:11:06 cri

A yau Alhamis 17 ga wata, a gun taron manema labaru, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, madam Hua Chunying ta yi bayani game da yanayin Ukraine cewa, bayan da ya yi shawarwari da takwaransa na Rasha, ministan harkokin waje na Sin, Wang Yi ya kara jaddada matsayin da Sin ta dauka na nacewa ga bin hanyar daidaita batun Ukraine a siyasance da samun daidaito tsakanin bangarori daban daban.

Madam Hua ta ce,a sa'i daya kuma, kasar Sin ta yi maraba da yin shawarwari tsakanin bangarori hudu da Rasha, Amurka, kungiyar tarayyar kasashen Turai, da ita kanta kasar Ukraine suke gudanar.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China