A wannan rana, Oleksander Turchynov da firaministan kasar Arseniy Yatsenyuk sun gana da mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden, bayan ganawarsu, Biden tare da Yatsenyuk sun kira taron manema labaru na hadin gwiwa, inda ya bayyana cewa, Amurka ba za ta amince da haramtaccen matakin da Rasha ta dauka na mamaye yankin Crimea har abada ba, a kokarinta, Amurka za ta ba da gudunmawa wajen dinke barakar kasar Ukraine gaba daya. Biden kuma ya kara da cewa, Amurka na ba da taimako ga Ukraine wajen warware matsalar makamashi, kuma za ta dauki matakan da suka dace don hana ko wace kasa da ta mayar da batun makamashi a matsayin makaman siyasa da za ta yi amfani da su a kan Ukraine da tarayyar Turai. Da yake tabo maganar kwaskwarima da za a yi kan siyasa da tattalin arzikin Ukraine, a cewarsa, Amurka na shirin baiwa Ukraine dalar Amurka miliyan 50 domin raya kasar daga dukkan fannoni. (Amina)