in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hargitsi ya yi sanadin rasa rayuka a gabashin Ukraine
2014-04-21 10:36:19 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fidda wata sanarwa ta shafin yanar gizonta a ranar Lahadi, in da ta ce an keta yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Rasha, da Amurka, da kungiyar kasashen Turai EU da Ukraine, sakamakon barkewar hargitsi a birnin Slavyansk dake gabashin Ukraine.

Hargitsin da ya auku da sanyin safiyar ranar Lahadi a cewar sanarwar, ya haddasa rasa rayuka tare da jikkata wasu jama'a da dama.

Dangane da hakan, gwamnatin kasar Rasha ta bayyana takaicinta, tana mai cewa lamarin ya shaida rashin aniyar mahukuntan Ukraine game da batun kwance damarar dakaru masu tsattsauran ra'ayi.

Daga Ukraine kuwa, ofishin ma'aikatar harkokin gidan kasar na jihar Donetsk, ya ba da labarin cewa, an yi musayar wuta a wajen birnin Slavyansk, lamarin da ya haddasa kisan wasu masu goyon bayan kafuwar 'Jamhuriyar Jama'ar Donetsk' guda 3, tare da raunata wasu su 3. Sai dai ba a tantance yawan mutanen da suka rasu, ko suka jikkata cikin wadanda suka ta da hargitsin ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China