A sakamakon karuwar tashe-tashen hankula a gabashin kasar Ukraine a 'yan kwanakin baya, shugaban majalisar Aleksandr Turchinov, wanda aka dora wa nauyin shugabancin kasar ya nuna a fakaice a ran 14 ga wata cewa, ba zai nuna adawa da kada kuri'ar raba gardama ba kan salon da kasar ke ciki, don tabbatar da kare gabashinta a cikin fadin kasar.
Hakazalika, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya yi nuni cewa, Rasha ba ta da sha'awar tada hankali a Ukraine, musamman sabo da cikakken yanki, da dinkuwar kasa, da daidaito a tsakanin jama'ar Ukraine sun dace da moriyar Rasha, amma ya kara da cewa, ya kamata a cimma burin ta hanyar yin gyare-gyare kan tsarin mulkin kasar. Ya kai suka ga mahukuntan Ukraine da su murkushe masu zanga-zanga da karfin soja a gabashin kasar, wanda ya lalata hadin gwiwar da kasa da kasa suke yi wajen samun sulhuntawa, haka kuma Lavrov ya kai suka ga kasashen yamma da su dauki ma'aunoni biyu yayin da suke la'akari da masu zanga-zanga a Kiv da gabashin Ukraine.
A ran 14 ga wata da dare kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya buga waya ga takwaransa na kasar Amurka Barack Obama, inda Putin ya yi kira ga Amurk da ta nuna kwarewa da take da ita, don kaucewa nuna karfin tuwo da ke haifar da zubar jini a kudu maso gabashin Ukraine.
Ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai wato EU sun shirya wani taro a ran 14 ga wata, inda suka cimma ra'ayi daya na kara sanyawa Rasha takunkumi. (Danladi)