kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin madam Hua Chunying ta bayyana hakan a Yyau Jumma'a 18 ga wata, a nan birnin Beijing, lokacin taron manema labarai da akan yi duk rana. kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin madam Hua Chunying ta bayyana cewa,
Sin ta yi maraba da cimma matsaya tsakanin Rasha, Amurka, kungiyar tarayyar Turai, da kuma Ukraine wajen don sassauna sassauta yanayin da ake ciki a Ukraine.
Madam Hua ta furta cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin dakae a kan matsayinta na ganin an daidaita batun Ukraine ta hanyar siyasa, ta yadda za'a samu zaman jituwa tsakanin al'ummomin kasar baki daya. Jami'ar ta cigaba datTa yi bayanin cewa a don haka kasar Sin na fatan bangarorin daban daban za su yi kokari tare, su dauki hakikanin hakikanan matakai, da tabbatar da matsaya da suka cimma, domin sa kaimi ga daidaita wannan matsala ta hanyar siyasa, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar cigaban kasar Ukraine tun da wuricikin lokaci.(Fatima)