A ran 6 ga wata, jama'a na jihohi uku da ke gabashin kasar Ukraine sun yi wata gagarumar zanga-zanga, inda suka bukaci kafa tsarin tarayya a Ukraine, masu zanga-zanga sun rushe babban gini na gwamnati sa'an nan suka mamaye shi. A ran 15 ga wata, Ukraine ta dauki matakan soja don magance matsalolin gabashin kasar, wannan dai ya jawo hankulan kasa da kasa.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya buga waya ga babban sakataren MDD Ban Ki-Moon a ran 15 ga wata, inda ya karfafa cewa, Rasha na sa ran ganin MDD da kasashen duniya su kai suka a fili ga ayyukan mahukuntan Ukraine da ke saba wa tsarin mulkin kasar.
A wannan rana kuma, firaministan Rasha Dmitry Medvedev ya yi nuni cewa, Ukraine ta kusan shiga cikin yakin basasa.
Kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka Jen Psaki ta bayyana a kwanan nan cewa, tun da dakarun sun fara harzuka a gabashin kasar, tilas ne gwamnatin kasar ta mayar da martani. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Amurka ta sake barazanar cewa za ta sanya wa Rasha takunkumi a ran 15 ga wata.
Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya yi nuni a ran 15 ga wata cewa, kungiyar za ta inganta hadin kai da kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU da sauran muhimman abokai. Ban da wannan kuma, kungiyar EU ta bayar da wata sanarwa a ran 15 ga wata cewa, EU ta yanke shawarar haramtawa tshofaffin jami'an Ukraine 4 yin amfani da kudaden da suka ajiye a banki. (Danladi)