A 'yan kwanakin baya, wasu jama'ar jihohin Donetsk, da Kharkiv, da kuma Luhanska dake gabashin Ukraine, sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga kasar Rasha. Sai dai a baya bayan nan halin da ake ciki a wadannan jihohi na kara tabarbarewa.
Hakan ne ma ya sanya shugaban majalisar dokokin kasar Ukraine Oleksander Turchynov, wanda ke rikon mukamin shugabancin kasar, ya sanar da cewa, kwamitin kula da zaman lafiya da tsaron kasar Ukraine ya yanke shawarar daukar matakan soja, a yaki da ta'addanci da ake yi a gabashin kasar.
Turchynov ya karfafa cewa, kasar ba za ta yarda Rasha ta sake daukar irin matakan da ta dauka a Crimea a yankunan gabashin kasar ba.
Game da kara tabarbarewar halin da ake ciki a Ukraine, zaunanniyar wakiliyar Amurka da ke MDD Samantha Power ta bayyana a ran 13 ga wata cewa, idan ba a samu sassauci kan halin da ake ciki a gabashin Ukraine ba cikin 'yan kwanaki masu zuwa, tabbas Amurka za ta duba yiwuwar kara sanya wa Rasha takunkumi. Ban da wannan kuma, gwamnatin Amurkan ta sanar a ran 12 ga wata cewa, mataimakin shugaban kasar Joseph Biden zai kai ziyara Ukraine a ranar 22 ga wata.
Kaza lika a ranar 13 ga watan nan ma, babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, ya yi kira ga Rasha da ta gaggauta daukar matakan sassauta halin da ake ciki, ta kuma janye sojojinta, da dakarun ta na musamman daga kasar Ukraine.
A nata bangaren kuma, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana a ranar 13 ga wata cewa, halin da ake ciki a kudu maso gabashin Ukraine yana dada tabarbarewa matuka, kuma Rasha ta riga ta gabatar da wannan batu gaban kwamitin sulhu na MDD, da kungiyar kula da harkokin tsaro da hadin kai ta Turai domin gudanar da shawarwari kan hakan. (Danladi)