Tsohon shugaban hukumar kula da ajiyar kudi na kasar Amurka Alan Greenspan ya ce, farashin hannayen jari na kasashen duniya zai ci gaba da faduwa kamar a makon da ya gabata, kuma ba za a farfado da kasuwannin kasashen duniya cikin sauri ba. Manazarcin kamfanin kula da harkokin saka jari na Moody na Amurka ya ce, game da rashin tabbas na kasuwannin kasashen duniya, hannayen jari na duniya zai ci gaba da faduwa. Amma an yi hasashen cewa, faduwar da aka samu ba za ta dauki wani dogon lokaci ba. Haka kuma, kamfanin Standard & Poor's na Amurka ya ce, a cikin wani dan kankanin lokaci, farashin hannayen jari zai ci gaba da faduwa, amma makomar hannayen jari za ta danganta ga tattalin arzikin Amurka, idan tattalin arzikin kasar bai samu koma baya ba, ba za a ci gaba da samun tsawwaluwar farashi ba.(Bako)