A lokacin muhawarar, mataimakin babban sakatare mai kula da harkokin kare hakkin dan Adam na MDD Ivan Simonovic ya yi bayani kan rahoton da ofishin kula da harkokin hakkin dan Adam na musamman ya fitar a ran 15 ga wata. Ya ce, hirar da ya yi tare da wakilan kananan hukumomin kasa, kungiyoyi masu zaman kansu da wasu fararen hula da dai saurasu, yayin da ya kai ziyarar aiki a kasar Crimea tun ranar 21 zuwa ta 22 ga watan Maris, kuma labaran da ya samu sun nuna cewa, an keta hakkin dan Adam a yayin kuri'ar raba gardama da aka yi a Crimea a ran 16 ga watan Maris, ciki har da sarrafa kafofin watsa labaru da dai sauransu. Bugu da kari, akwai bukatar a gudanar da bincike game da yanayin hakkin dan Adam kan ayyukan zanga-zangar da ake yi a gabashin kasar Ukraine.
Haka kuma, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana cewa, kasar Sin na damuwa sosai game da tabarbarewar yanayin kasar Ukraine, tare da fatan bangarorin da abin ya shafa na kasar za su iya kai zuciya nesa, ta yadda za a hana kara tsanantar yanayi a kasar. (Maryam)