Kamata ya yi kasashen yammacin duniya su daina sa hannu cikin harkokin cikin gida na Ukraine, in ji ministan harkokin wajen Rasha
Jiya Jumma'a 4 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergey Lavrov ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, sabanin ra'ayin dakebambanci tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya kan daidaita rikicin Ukraine shi ne, ko gwamnatin Ukraine tana iyar girmamawa hakkin jama'ar dake wurare daban daban na kasar cikin adalci da 'yanci. Sergey Lavrov ya ce, idan ana fatan yin kwaskwarima a Ukraine, dole ne a yi kwaskwarima kan kundin tsarin mulkin kasar tukuna. Amma idan ana fatan cimma wannan buri, dole ne sauran kasashen duniya su daina sa hannu cikin harkokin cikin gida na kasar. Amma har zuwa yanzu, kasashen yammacin duniya suna ba da umurni ga Ukraine, shi ya sa Ukraine ba ta samu hakikanin 'yancinta ba.
Ban da haka, game da zargin da wasu jami'an gwamnatin Ukraine suka yiwa tsohon shugaban kasar Viktor F.Yanukovych na cewa, ya taba ba da umurni ga 'yan sanda da su harbe masu zanga-zanga a filin dake birnin Kiev, Sergey Lavrov ya ce, mahukuntan Kiev sun kyale sakamakon binkice kan wannan batu da aka gabatar a cikin kwanaki 15 da suka wuce, wannan ya haddasa kawo shakku kan abubuwan dake cikib binkicensa aka kasa samun wani hakikanin bayani. Ya kara da cewa, Rasha ba ta da hannu cikin wannan lamari, kuma ba zata goyi bayan irinsa ba. (Fatima)