A ranar 1 ga watan Afrilu, majalisar dokoki ta kasar Ukraine ta amince da kudurin da shugaban majalisar Aleksandr Turchinov, wanda aka dora wa nauyin shugabancin kasar, ya gabatar, dake baiwa sojojin kasashen waje damar shiga Ukraine a shekarar bana don yin atisayen soja.
A ranar kuma, Amurka da Ukraine sun yi shawarwari kan tsaro a birnin Kiev, kakakin ma'aikatar tsaron Amirka wato Pentagon Steve Warren ya karfafa cewa, sojojin Amurka sun kara karfin tsaro a yankunan da ke kewayen kasar Rasha. Ban da wannan kuma, a ranar 1 ga wata, majalisar wakilai ta kasar Amurka ta zartas da kuduri na ba da taimako ga Ukraine, ta fuskar tattalin arziki da kuma sanya takunkumi ga Rasha sakamakon matsalar Crimea.
A ranar 1 ga wata kuma, kungiyar tsaro ta NATO da Ukraine sun bayar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka bayyana cewa, kungiyar NATO ta yanke shawarar dakatar da dukkan ayyukan hadin kai da Rasha irin na jama'a da sojoji, NATO za ta yi mu'ammala da Rasha bisa tsarin kwamitin kula da harkokin NATO da Rasha, domin daidaita rikicin Ukraine.
A nata bangare, majalisar dattawan kasar Rasha ta zartas da wani kudurin da shugaban kasar ya gabatar, da ya shafi soke yarjejeniyoyi huku kan jibge jiragen ruwa masu sunan bahar Aswad a tsakanin Rasha da Ukraine. (Danladi)