in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya damu da halin da ake ciki a gabashin Ukraine
2014-04-13 15:49:48 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a gabashin kasar Ukraine, ciki hadda rahoton aukuwar tashe-tashen hankula a baya bayan nan.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar a jiya Asabar, ya kara da cewa karuwar fadace-fadace ba zasu yiwa dukkanin bangarorin da abin ya shafa wani amfani ba.

A ranar ta Asabar ne dai aka bada rahoton cewa, wasu 'yan bindiga da ba a kaiga tantance ko su waye ba, sun kwace wani ofishin 'yan sanda a birnin Slavyansk, mai nisan kimanin kilomita 100 daga birnin Donetsk a gabashin kasar.

Jami'an tsaron yankin sun ce baya ga kwace ofishin, dakarun sun kuma kwace bindigogin 'yan sandan dake aiki a wurin.

(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China