Tun daga watan Maris, an rika samun aukuwar zanga-zanga a ranakun hutu a wasu sassan gabashin kasar ta Ukraine da suka hada da Donetsk da Kharkiv da kuma Luhansk, inda masu zanga-zangar suka ki amincewa da sabbin gwamnonin jihohin da aka nada bayan da aka kori Viktor Yanukovych, tare da bukatar kara ba wa sassan 'yanci da kuma bukatar jefa kuri'ar raba gardama a kan matsayinsu.
Jaridar Guardian ta labarta a wannan rana cewa, don sassauta halin da ake ciki a kasar ta Ukraine, kungiyar tarayyar Turai da Rasha da Amurka da Ukraine za su yi shawarwari a ranar Alhamis mai zuwa. Har wa yau, John Kerry, sakataren harkokin waje na Amurka ya sake musanta yiwuwar daukar matakan soja dangane da batun Ukraine, saboda a cewarsa, Amurkawa ba su son tsumduma cikin yaki kan batun Crimea.(Lubabatu)