Fadar shugaban kasar Amurka ta White House, ta ba da sanarwa a ran 12 ga wata cewa, mataimakin shugaban kasar Joseph Biden zai gudanar da ziyarar aiki a birnin Kiev hedkwatar kasar Ukraine.
Sanarwar ta ce, Biden zai tattauna da jami'an Ukraine yayin zaiyarar da zai gudanar ran 22 ga watan nan, musamman kan yadda za su yi amfani da tasirin al'ummar duniya, wajen kiyaye tattalin arzikin kasar ta Ukraine.
Ban da haka kuma, bangarorin biyu za gudanar da shawarwari kan yadda Ukraine za ta kyautata tsarin mulkinta, da batun babban zaben da za ta yi a watan Mayu mai zuwa. Har wa y au sanarwar ta bayyana cewa, ziyarar Biden a wannan karo za ta bayyana goyon bayan Amurka ga kasar ta Ukraine.
A wani ci gaban kuma ministan harkokin cikin gidan kasar Ukraine Arsen Avakhov, ya bayyana a wani shafin sa na yanar gizo cewa, gwamnatin kasar za ta dauki tsattsauran mataki kan dakarun nan da suka mamaye wani ofishin 'yan sanda a birnin Slaviansk a safiyar ranar Asabar.
Ya ce, tuniA nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya tattauna da takwaransa na kasar Amurka John Kerry ta wayar tarho, idan inda ya Kerry ya bayyana amfani da karfin tuwo a kudu maso gabashin kasar Ukraine, a matsayin matakin da zai kawo babban cikas, ga makomar sulhunta takaddamar kasar ta Ukraine, ciki hadda batun shawarwarin da Rasha, da Amurka, kungiyar EU ke yi da Ukraine.
Bugu da kari, ma'aikatar harkokin waje kasar Rasha ta ba da sanarwa cewa, Kerry ya damu kwarai kan zanga-zangar da ake yi a kudu maso gabashin kasar ta Ukraine. Yana mai ra'ayin cewa zuga mutane aka yi su yi bore, kuma Rasha ce ke da hannu a aikita hakan. Kaza lika Mr. Kerry ya jaddada cewa, kamata ya yi Rasha ta janye mutanen da ta girke a wannan wuri. (Amina)