A wannan rana kuma, babban sakataren kungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika ta NATO Anders Rasmussen ya bayyana cewa, kungiyar za ta karfafa aikin soja a tsakaninta da mambobi kasashen kungiyar dake makwabtaka da kasar Rasha, inda ya kuma yi kira ga mambobi kasashe da su kara kasafin kudinsu wajen aikin soja. Ya kai ziyarar aiki a kasar Bulgaria a wannan rana, inda ya jaddada bukatun karfafa hadin gwiwar mambobi kasashen kungiyar NATO kan aikin soja, da kuma kara kasafin kudi kan aikin don samun kayayyakin soja na zamani, bayan ganawarsa da shugaban kasar.
A 'yan kwanan na baya baya, ana fama da tashe-tashen hankula a yankunan dake gabashi da kuma kudancin kasar Ukraine, inda wasu yankunan kasar suke fafutukar neman 'yancin kansu domin shiga tarayyar kasar Rasha ta hanyar kuri'ar raba gardama. (Maryam)