Da safiyar Lahadin nan ne al'ummun yankin Crimea na kasar Ukraine, suka gudanar da kuri'ar jin ra'ayi, kan matsayar yankin ta kodai ci gaba da kasancewa a Ukraine, ko kuma komawa karkashin ikon kasar Rasha.
Ana dai saran kammala jefa kuri'ar ne da misalin karfe 8 na dare, bisa agogon wurin.
A cewar shugaban kwamitin gudanar da zaben yankin na Crimea Mikhail Malyshev, mai yiwuwa ne a gabatar da sakamakon zaben a gobe Litinin.
Baya ga batun makomar yankin, kuri'ar za ta kuma bayyana matsayar al'umma kan batun maido da tsarin mulkin jamhuriyyar Crimea na shekarar 1992, da matsayin Crimea na wani yankin kasar Ukraine. (Amina)