A wannan rana kuma, kotun kasar Ukraine ta ba da umurnin cafke firaminista da shugaban majalisar dokokin yankin na Crimea. Mukadashin babban mai gabatar da kara a kotu na kasar Ukraine Oleg Magnitsky ya bayyana cewa, sun riga sun daukaka karar da aka shigar kan laifuffukan da ake tuhumar firaminista da shugaban majalisar dokoki da wasu manyan jami'ai na yankin Crimea da aikatawa.
A Jiya Laraba 5 ga wata ne, ministan harkokin wajen kasar Rasha wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a kasar Spain, ya bayyana cewa, aiwatar da yarjejeniyar da gwamantin kasar Ukraine ta kulla tare da jam'iyyar adawa a ran 21 ga watan Fabrairu yadda ya kamata, shi ne muhimmin mataki a halin yanzu wajen warware rikicin kasar Ukaraine. Ya kuma yi tir da sakacin da kasashen yamma ke yi, tare da rashin daukar matakai cikin hanzari, game da batun keta ikon kasar Ukraine. (Maryam)