Har wa yau a dai wannan rana ita ma majalisar dokokin birnin Sevastopoli, wadda daya ne daga cikin birane biyu da kai tsaye ke karkashin mulkin babbar gwamnatin kasar Ukraine, ta tsaida kudurin cewa, birnin zai shiga tarayyar kasar Rasha.
Dangane da hakan, shugaban majalisar dokokin kasar Ukraine, wanda a halin yanzu ke matsayin shugaban wucin gadin kasar Alexander Turchynov, ya bayyana a jiya 6 ga wata da dare cewa, bisa ikon da dokokin mulkin kasar suka ba shi, ya dakatar da kudurin majalisar dokokin yankin na Crimea, kuma majalisar dokokin kasar Ukraine za ta rushe majalisar dokokin yankin Crimea.
A nasa bangare shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ba da wata sanarwa a ranar 6 ga watan, inda ya nuna cewa, jefa kuri'ar raba gardama da za a gudanar dangane da makomar yankin na Crimea bai dace da tsarin mulkin kasar Ukraine ba, ya kuma sabawa dokokin kasa da kasa ba. Ya ce ya zama dole a tattauna kan harkokin da suka shafi kasar ta Ukraine, tare da gwamantin kasar ta halal.
Mr. Obama ya kara da cewa, ya riga ya ba da umurnin kakaba wa wadanda suka sa hannu cikin batun yankin na Crimea takunkumi, da ya hada da dakatar da ba su bizar shiga kasar Amurka, da kuma rike kudade, da kadarorinsu dake Amurkan. Har wa yau majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da wani daftarin doka, da zai baiwa kasar ta Ukraine damar samun rancen kudi har dallar Amurka biliyan 1.
Bugu da kari a dai wannan rana, kwamitin tarayyar kasar Rasha, da kuma majalisar wakilan kasar sun bayyana cewa, ba zu su bayyana matsayansu kan batun yankin na Crimea ba, sai bayan yankin ya kammala aikin kada kuri'un daukacin jama'ar sa.
A hannu guda kuma shugaban kasar Rasha ya jagoranci wani taro na kwamitin tsaron tarayyar kasar, inda aka tattauna kan matakan da za su dace kasar ta dauka, dangane da kudurin da majalisar dokokin yankin Crimea ta gabatar na shiga tarayyar kasar Rasha, sai dai bai yi karin haske don gane da taron ba. (Maryam)